Makarantar Waniltu Tayi Bikin Kaddamar Da Sabbin Daliban Solar

 Wannan Matar Da Mijinta Sunyi Faɗa, Don Haka Mijin Ya Raba Gidan Tsagi Biyu Yace Daga Yanzu Ta Tsaya A Bangarenta, Shima Ya Tsaya A Nashi, Duk Wanda Ya Taka Dokar Nan Kuma Zai Biya Kuɗi Ko Ya Fuskanci Shari'a.



Ita Kuma Matar Ta Yarda, Tayi Tsammanin Haka Abin Yake Da Sauƙi, Harma Ta Ƙara Da Cewa Duk Wanda Ya Ƙetara Iyaka, Zai Bar Gidan Gabadaya. Mijin Ya Tsaya Yayi Tunani Amma Daga Baya Yarda Da Hakan.

Har Zai Yi Kuskuren Ketare Hannunsa Zuwa Ɓangarenta Amma Ya Gano Yaudararsa Zatayi Ya Dakata.

Sai Dai Kuma Matsalar Asalin Kofar Fita Daga Dakin Yana Ɓangaren Matar Ne, Sai Ta Tambaye Shi Taya Zai Fita Waje,

Mijin Kuma Ya Dubi Taga Yace Zai Fita Ta Window,

Daga Nan Ya Sake Faɗa Mata, Ban Ɗaki Yana Ɓangarensa, Zai Ga Yadda Zatayi. Ita Kuma Tace Zata Iya Zuwa Gidan Makwabta Ai.

Ba'a Jima Ba, Matar Ta Gano Computer Mijin A Ɓangarenta, Daga Nan Ta Ɗauko Shi Ta Pasa Shi, Minin Ya Gagara Rike Fushinsa Don Haka Shima Ya Ɗauko Kayanta Mai Tsada Ya Yanka Da Almakace, Daga Nan Faɗa Ya Ɓarke Tsakaninsu.

Sai Dai A Wannan Lokacin Ne Mai Gidansa Ya Kira, Amma Rashin Sa'a Wayar Na Ɓangaren Matar, Sai Ta Amsa Wayar Ta Yiwa Mai Gidan Nashi Ihu Sa'annan Ta Kashe Wayar.

A Fusace Mijin Yace Shikenan Ya Rasa Aikinsa, Amma Duk Da Haka Bai Ketare Bordan Ban.

Suna Cikin Surutu Jaririnsu Ya Tashi Daga Bacci, Matar Tayi Tsammanin Yunwa Yake Ji, Sai Dai Kuma Madarar Jaririn Yana Ɓangaren Mijin, Ta Manta Da Komai Ta Ketare Bodan Ta Ɗauko Gorar Madarar, Shikuma Mijin Bai Ce Komai Ba.

Tayi Ta Rarrashin Jinjirin Amma Bai Daina Kuka Ba. Ganin Hakane Yasa Mijin Shima Ya Ƙetara Borda Ya Karɓi Jaririn Sa'annan Suka Rarrashe Shi Tare Yayi Shiru.

Idan Kaine Mijin Ko Kece Matar Zaka Hakura Kuwa, Ko Za'a Cigaba Da Yaƙin.

Comments